logo

HAUSA

Sin Ta Yi Allah Wadai Da Dokar Da Amurka Ta Kafa Mai Lakabin “Haramta Tilastawa Al’ummar Uygur Kwadago”

2021-12-24 20:14:49 CRI

Sin Ta Yi Allah Wadai Da Dokar Da Amurka Ta Kafa Mai Lakabin “Haramta Tilastawa Al’ummar Uygur Kwadago”_fororder_xj

Wata sanarwar da ma’aikatar kasuwancin kasar Sin ta fitar, ta yi tir da matakin Amurka, na zartar da dokar da ta kira “haramta tilastawa al’ummar Uygur kwadago”, tana mai bayyana ta, a matsayin cin zali ta fuskar tattalin arziki.

Sanarwar wadda aka fitar a Juma’ar nan, ta ce karkashin dokar, an lissafa dukkanin hajoji da ake samarwa a jihar Xinjiang, a matsayin wadanda ake sarrafawa ta hanyar aikin tilas. Kaza lika ta tanaji haramcin shigar da hajojin da aka sarrafa a Xinjiang cikin Amurka.

Cikin martanin da ta mayar, ma’aikatar kasuwancin Sin ta ce, Amurka ta fake da batun kare hakkin bil Adama wajen aiwatar da manufofin kebe kai, da baiwa kasuwa kariya da cin zali, wanda hakan ya yi matukar karya ka’idojin kasuwanni, ya kuma sabawa dokokin kungiyar cinikayya ta duniya WTO.

Har ila yau, matakin na Amurka ya yi matukar lahanta moriyar sassan kasuwancin kasar Sin, da ma moriyar masu sayayya na Sin da Amurka, kana ya lahanta yanayin daidaito a ayyukan samar da hajojin masana’antun kasa da kasa, da ma matakan farfadowar tattalin arzikin duniya. Daga nan sai ma’aikatar kasuwancin na Sin, ta bayyana matukar rashin amincewa, da kakkarfar adawa da matakin muzgunawar Amurka ta wannan fanni na tattalin arziki.   (Saminu)

Saminu