logo

HAUSA

Neman Ci Gaban Bai Daya Abu Ne Da Ya Dace Sin Da Amurka Su Maida Hankali A Kai

2021-12-22 20:24:43 CRI

Neman Ci Gaban Bai Daya Abu Ne Da Ya Dace Sin Da Amurka Su Maida Hankali A Kai_fororder_sindaAmurka

Jakadan kasar Sin a Amurka Qin Gang, ya ce kamata ya yi Sin da Amurka, su maida hankali ga aiwatar da manufofin samar da ci gaban bai daya. Qin wanda ya yi wannan tsokaci yayin liyafar shekara-shekara da ake gudanarwa, karkashin dandalin tsara manufofi na Sin da Amurka, wanda aka gudanar a jiya Talata, ya ce ci gaba mai dorewa, da daidaiton tattalin arziki da Sin ke samu a yanzu, ba barazana ba ce ga Amurka, maimakon hakan, wata babbar dama ce ta samar da moriya.

Burin wanzar da ci gaban Sin shi ne biyan bukatun al’umma, ba wai shiga wata takarar yada-kanin wani ba. Qin ya kara da cewa, cikin ‘yan shekarun baya bayan nan, alakar Sin da Amurka ta fuskanci wasu wahalhalu, kuma hakan ba shi ne burin al’ummun kasashen 2 ba.

Qin ya ce, "Muna fatan Amurka za ta martaba ‘yancin al’ummun kasar Sin na neman samun rayuwa mai yalwa, ta kuma rungumi salon ci gaban kasar Sin".   (Saminu)

Saminu