logo

HAUSA

Rasha ta fice daga yarjejeniyar bude sararin samanta a hukumance

2021-12-19 17:23:55 CRI

Ma’aikatar harkokin wajen kasar Rasha ta sanar da cewa, kasar ta fice daga yarjejeniyar bude sararin saman kasashen duniya wato Treaty on Open Skies, a hukumance.

Sanarwar ta ce, nasarar shafe gomman shekaru da aiwatar da yarjejeniyar, ta nuna cewa, yarjejeniyar ta yi tasiri matuka a matsayin wata hanyar inganta tabbatar da tsaro da amincewa da juna, da samar da karin damammaki ba tare da nuna rashin adalci ba wajen nazartar ayyukan soji a tsakanin kasashen dake karkashin yarjejeniyar.

Ma’aikatar ta bayyana cewa, a lokacin da Rasha ta shiga yarjejeniyar, kasar ta gudanar da zirga-zirgar jiragen sama sau 646, kana ta bayar da damar zirga-zirgar jiragen sama ta yankunanta sau 449 daga cikin adadin jimillar zirga-zirgar jiragen saman 1,580 da aka gudanar.

Sai dai ba zato ba tsammani, dukkan kokarin da kasar ta yi na ganin dorewar ci gaba da zamanta karkashin yarjejeniyar ya ci tura, kamar yadda sanarwar ta bayyana.

A cewar ma’aikatar, kasar Amurka ce ta dauki dukkan alhakin saba wa yarjejeniyar, wadda ita ce ta kirkiri kulla yarjejeniyar ta Treaty on Open Skies.

Bayan da Amurka ta janye daga yarjejeniyar a hukumance a watan Nuwamban shekarar 2020, ma’aikatar harkokin wajen Rashan ta ce daga watan Janairun wannan shekara kasar ta fara shirye-shiryen fita daga yarjejeniyar a hukunmance. A ranar 7 ga watan Yuni, shugaban kasar Rasha Vladimir Putin ya sanya hannu kan ficewa daga yarjejeniyar.(Ahmad)

Ahmad