logo

HAUSA

Zhao Lijian: Amurka ce kan gaba wajen yiwa kasashen duniya matsin lambar tattalin arziki

2021-12-22 20:16:13 CRI

Zhao Lijian: Amurka ce kan gaba wajen yiwa kasashen duniya matsin lambar tattalin arziki_fororder_赵立坚

Mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Zhao Lijian, ya ce kasar Amurka ce ke kan gaba, wajen yiwa sauran kasashen duniya matsin lamba ta fuskar tattalin arziki.

Zhao Lijian, wanda ya bayyana hakan a Larabar nan, yayin da yake martani ga kalaman da sakataren harkokin wajen Amurka Antony Blinken ya yi, lokacin wata zantawarsa da firaministar Lithuania Ingrida Simonyte.

Yayin zantawar da suka yi ta wayar tarho, Mr. Blinken ya zargi hukumar kwastam ta kasar Sin, da kin baiwa hajojin kamfanonin Lithuania, ko kayayyakin da aka hada da sassan kayan kamfanonin kasar damar shiga Sin. Yana mai cewa, hakan wani matsin lamba ne irin na tattalin arziki da Sin ke yawa Lithuania.

To sai dai kuma a martanin sa, Mr. Zhao ya karyata zargin na Blinken, yana mai cewa, burin Amurka shi ne haddasa fito na fito tsakanin Sin da Lithuania.

Jami’in na Sin ya kara da cewa, Amurka ta yi amfani da batun tsaron kasa wajen karya dokar cinikayya, tare da kitsa karairayi domin dakile ci gaban kamfanonin wasu kasashe. Daga nan sai ya yi kira ga mahukuntan Lithuania, da su fuskanci hakikanin batun da ake magana a kai, game da cudanyarta da kasar Sin, tare da gyara kuskuren ta.   (Saminu)

Saminu