logo

HAUSA

Dan tayi daya yana mutuwa a ko wadanne dakikoki 16 a lokacin haihuwa a duniya

2021-09-04 18:37:51 CRI

Asusun kula da kananan yara na MDD UNICEF, hukumar lafiyar ta duniya WHO, Bankin Duniya da sashen kula da yawan mutane na MDD sun kaddamar da rahoto na farko na hadin gwiwa dangane da batun yadda ‘yan tayi ke mutuwa a lokacin haihuwa, inda suka nuna cewa, a ko wace shekara, ‘yan tayi kimanin miliyan 2 ne suke mutuwa a lokacin haihuwa a duniya, inda aka yi kisayin cewa, dan tayi daya yana mutuwa a cikin ko wadanne dakikoki 16 a lokacin haihuwa a duniya. Barkewar annobar cutar numfashi ta COVID-19 ta kara tsananta irin wannan halin da ake ciki a duniya.

Wannan rahoto mai lakabin “abin tausayi da aka kau da kai: mutuwar ‘yan tayi” ya yi bayani da cewa, alkaluman kididdiga sun shaida cewa, yawancin ‘yan tayin dake mutuwa a lokacin haihuwa sun danganta da rashin kulawa mai dacewa a lokacin samun ciki da kuma lokacin haihuwa. Manyan kalubalolin da ake fuskanta yanzu su ne, rashin isassun hidimomin da ake bai wa masu juna biyu kafin haihuwa da kuma a lokacin haihuwa, da matsalar karancin aikin horaswa da zuba jari kan majiyyata da ungozoma.

Tedros Adhanom Ghebreyesus, babban dakataren hukumar WHO ya yi nuni da cewa, mutuwar ‘yan tayi a lokacin haihuwa, mai ban tausayi ta nuna muhimmancin inganta da tabbatar da ba da hidimar kiwon lafiya ta tilas, da kuma kara zuba jari kan majiyyata da ungozoma.

Alkaluman kididdiga sun nuna cewa, mutuwar ‘yan tayi a lokacin haihuwa da yawansu ya kai kaso 84 cikin 100 suna faruwa ne a kasashe masu karancin kudin shiga da kuma kasashe masu karanci da matsakaicin kudin shiga. Ban da haka kuma, a dukkan kasashe masu karancin kudin shiga da kuma kasashe masu yawan kudin shiga, yawan mutuwar ‘yan tayi a lokacin haihuwa ya fi yawa a yankunan karkara, gwargwadon yadda lamarin yake a birane. Rahoton ya kara da cewa, ana iya magance mutuwar ‘yan tayi a lokacin haihuwa ta hanyar ba da kulawa mai dacewa cikin hanzari. A yankunan nahiyar Afirka da ke kudu da hamadar Sahara da yankin tsakiyar Asiya da kuma yankin kudancin Asiya, mutuwar ‘yan tayi a lokacin haihuwa ta fi yawa gwargwadon a nahiyar Turai, arewacin nahiyar Amurka, kasashen Australiya da New Zealand.

Madam Zhang Chuji, wata likita ce da ke aiki a asibitin Tiantan na Beijing ta gaya mana cewa, ko da yake an samu ci gaba wajen daukar matakan kiwon lafiyar kananan yara don yin rigakafin mutuwarsu, amma saurin raguwar mutuwar ‘yan tayi a lokacin haihuwa bai yi daidaita da hasashen da mutane ke yi ba. Yawan mutuwar ‘yan tayi a lokacin haihuwa ya ragu da kaso 2.3 cikin 100 ne kawai a kowace shekara daga shekarar 2000 zuwa 2019. Rahoton ya kuma yi gargadi da cewa, barkewar annobar cutar COVID-19 ta tsananta halin da ake ciki a duniya. An yi kiyasin cewa, barkewar annobar ta rage rabin hidimomin lafiya da ake bayar wa a duniya. Nan da watanni 12 masu zuwa, ana hasashen za a samu karin mutuwar ‘yan tayi kusan dubu 200 a lokacin haihuwa a kasashe masu karancin kudin shiga da kasashe masu matsakaicin kudin shiga guda 117.(Tasallah Yuan)

Tasallah Yuan