logo

HAUSA

An kafa sama da asibitoci 1,600 ta kafar intanet a kasar Sin

2021-08-21 16:30:50 CMG

An kafa sama da asibitoci 1,600 ta kafar intanet a kasar Sin_fororder_0821-Asibiti-Faeza

Hukumar kula da lafiya ta kasar Sin, ta ce kawo yanzu, an kafa sama da asibitoci 1,600 ta kafar intanet a kasar, inda aka duba tare da jinyar mutane kusan miliyan 49 a shekarar 2020.

Mataimakin daraktan hukumar Yu Xuejun, ya bayyana a jiya yayin wani taron kiwon lafiya a bikin baje kolin Sin da kasashen Larbawa dake gudana a jihar Ningxia ta arewa maso yammacin kasar Sin cewa, inda aka kaddamar da sabon tsarin na kiwon lafiya ta kafar intanet na farko.

Ya ce samar da kiwon lafiya ta kafar Iintanet ya zama wata muhimmiyar alkibla da kasashe da dama suka dauka domin samar da sauyi da daukaka tsarin kiwon lafiya, kuma kasar Sin na matukar kokarin hada fasahar sadarwa da ayyukan tsafta da na kiwon lafiya.

Ya kuma bayyana cewa samar da kiwon lafiya ta kafar intanet ya zama wani bangare mai matukar muhimmaci, kana an ga fa’idojinsa, kamar na rashin mu’amala ta kai tsaye, yayin da ake yaki da cutar COVID-19 a kasar Sin. (Fa’iza Mustapha)

Faeza