logo

HAUSA

Mutane 24 sun mutu sanadiyyar gubar abinci a arewa maso yammacin Nijeriya

2021-08-11 11:02:43 CMG

Mutane 24 sun mutu sanadiyyar gubar abinci a arewa maso yammacin Nijeriya_fororder_1

Mutane 24 sun mutu sannadiyyar cin abincin da aka dafa da wani nau’in sinadarin taki, a jihar Sokoto dake arewa maso yammacin kasar.

Kwamishinan lafiya na kasar Ali Inname, ya bayyana cikin wata sanarwa cewa, lamarin ya auku ne a kauyen Danzake dake yankin karamar hukumar Isa ta jihar a ranar Litinin, bayan mutane 24 daga wani babban gida a kauyen, sun ci abincin da aka dafa da wani nau’in sinadarin taki, wanda suka dauka gishiri ne.

A cewarsa, mutane 24 na gidan da suka ci abincin sun rasa rayukansu, in banda mata biyu da dandana abincin kawai suka yi, kuma yanzu haka suna samun kulawa, kana ana kyautata zaton za su rayu.

Ya kuma yi kira ga mutanen kauyen su dauki darasi daga wannan lamari, su rika boye sinadarai masu guba. (Fa’iza Mustapha)

Fa'iza