logo

HAUSA

Kasar Sin ta jinjinawa hadin kai da amincin taron hadin kan kasashen gabashin Asiya

2021-08-08 16:09:39 CRI

Ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin ta jinjinawa kyakkyawan yanayin da tarukan hadin kan kasashen gabashin Asiya suka kasance ciki, inda ta jaddada muhimmancin aminci da hadin kai da goyon baya a tsakanin kasashen.

Wannan na zuwa ne bayan mamban majalisar gudanarwar kasar Sin, kuma ministan harkokin wajen kasar Wang Yi, ya kammala halartar jerin tarukan hadin kan kasashen gabashin Asiya a ranar Juma’a.

Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin madam Hua Chunying, ta ce hadin gwiwa wajen yaki da annobar cutar numfashi ta COVID-19 shi ne babbar matsayar da ministocin harkokin wajen kasashen suka cimma.

Ta kara da cewa, dukkan bangarorin sun amince cewa, aiki na gaggawa a yanzu shi ne, karfafa hadin gwiwa kan samar da rigakafi da kuma inganta hanyoyin samar da shi kan farashi mai rahusa.

A cewarta, Wang Yi ya nanata alkawarin kasar Sin na mayar da rigakafin matsayin hajar da dukkan al’ummar duniya za su samu, da kuma kudurin Sin din, na hada hannu da kasashen yankin wajen cimma bukatun rigakafin na bai daya.

Har ila yau, madam Hua Chunying ta ce, kasashe da dama sun bayyana goyon bayansu ga matsayin kasar Sin dangane da binciken asalin cutar, wato batu ne na kimiyya da ya kamata ya kasance karkashin ka’idojin da batun ya shafa, tare kuma da kaucewa siyasantar da shi.

A daya bangaren kuma, dukkan bangarorin sun amince cewa, akwai rashin daidaito a fannin farfado da tattalin arzikin yankin, lamarin da ya sa sabbin kalubaloli ke kara bullowa.

A cewar kakakin, ya kamata kasashen yankin sun yi aiki tare da zurfafa hadin gwiwar da ke tsakaninsu domin kara karfinsu na tunkarar matsaloli.

A lokaci guda kuma, ta ce, ya kamata kasashen su mayar da hankali kan inganta dabarun hadin kai da inganta juriya da karfin hadin gwiwa mai dorewa a yankin, tare da ci gaba da tabbatar da dorewar kwanciyar hankali da zaman lafiyar da aka sha wahalar samu. (Fa’iza Mustapha)

Fa’iza Mustapha