logo

HAUSA

Kasar Sin Ta Bukaci Kasashen Duniya Su Rika Aiwatar Da Hulda Ta Gaskiya

2021-07-03 20:14:09 CRI

Kasar Sin Ta Bukaci Kasashen Duniya Su Rika Aiwatar Da Hulda Ta Gaskiya_fororder_wy

Ministan harkokin wajen kasar Sin, kuma mamban majalisar gudanarwar kasar Wang Yi, ya yi kira ga kasashen duniya da su daukaka tare da aiwatar da hulda ta gaskiya a tsakaninsu, domin tunkarar kalubalen tsaro daban-daban yadda ya kamata.

Wang Yi ya bayyana haka ne a yau Asabar, yayin da yake jawabin bude taro kan zaman lafiyar duniya karo na 9, a Jami’ar Tsinghua ta Beijing.

Taron wanda jami’ar ta shirya da hadin gwiwar cibiyar nazarin harkokin kasashen waje ta kasar Sin, na mayar da hankali ne kan tabbatar da tsaro a duniya. Taken taron a bana shi ne hadin kan kasa da kasa kan tsaro bayan wucewar annobar COVID-19: daukakawa da aiwatar da hulda tsakanin kasa da kasa.

Wang Yi ya kuma yi kira ga dukkan kasashe su hada hannu wajen tunkarar kalubalen duniya da inganta sulhunta batutuwa ta hanyar siyasa da kuma adawa da munanan dabi’un dake kawo rarrabuwar kawuna da fito na fito.

A cewarsa, kasar Sin za ta daukaka kyawawan dabi’u da nacewa ga hadin gwiwa na hakika, da aiwatar da sabuwar dabarar tabbatar da tsaro da hada hannu da sauran kasashe wajen samar da zaman lafiya na bai daya, kuma mai dorewa a duniya. (Fa’iza Mustapha)

Fa’iza Mustapha