logo

HAUSA

Sama da mutane 200 sun ji rauni a taho mu gaman jiragen kasa a Kuala Lumpur

2021-05-25 10:26:58 CRI

Sama da mutane 200 sun ji rauni a taho mu gaman jiragen kasa a Kuala Lumpur_fororder_1127486816_16218903095001n

Rahotanni sun bayyana cewa sama da mutane 200 ne suka samu raunuka, daga cikinsu mutane 47 sun samu raunuka masu tsanani, yayin da jiragen kasa biyu suka yi taho mu gama sakamakon sauka daga kan hanyarsu a babban birnin kasar Malaysia, Kuala Lumpur a jiya Litinin.

Lamarin ya faru ne da misalin karfe 8:30 na yamma agogon kasar yayin da wani jirgin kasa wanda babu mutane cikinsa ya yi taho mu gama da wani jirgin kasan mai dauke da mutane 232 a hanyar jirgin kasan na Kelana Jaya Light Rail Transit (LRT) dake zirga-zirga a cikin birnin, a kusa da tashar KLCC ta karkashin kasa dake wajen ginin Petronas Towers, kafofin yada labaran kasar sun bada rahoton cewa ministan sufurin kasar Malaysia Wee Ka Siong, shi ne ya bayyana hakan.

Ministan ya fadawa taron manema labarai cewa jirgin kasan wanda babu mutanen cikinsa yana gudanar da aikin gwaji ne.

Ya ce, lamarin shi ne irinsa na farko da ya faru a tarihin kafuwar layin jirgin kasan birnin na LRT shekaru 23 da suka gabata, ya kara da cewa, an kafa kwamitin musamman domin gudanar da bincike kan abin da ya sabbaba taho mu gaman jiragen kasan.(Ahmad)

Ahmad