An bude sabon shafin hadin gwiwar Sin da Malaysia
2018-08-21 14:17:19 cri
Yau Talata, firaministan kasar Malaysia Mahathir Mohamad mai shekaru 93 ya kammala ziyararsa a kasar Sin, kuma wannan shi ne ziyararsa ta farko a kasar Sin bayan da ya sake hawa kan matsayin firaministan kasar Malaysia.
A yayin da yake ganawa da firaminista Mohamad, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya nuna yabo matuka kan goyon bayan da Mr. Mohamad yake baiwa kasar Sin kan raya shirin "Ziri daya da hanya daya", da kuma babbar gudummawar da ya bayar wajen inganta hadin gwiwar dake tsakanin kasashen Asiya baki daya. (Maryam)