logo

HAUSA

Xi Jinping ya gana da firaministan Malaysia

2018-08-21 11:16:15 cri

Jiya Litinin, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya gana da firaministan kasar Malaysia Mahathir Bin Mohamad a babban gidan sauke baki na kasar Sin na Diaoyutai dake birnin Beijing.

A yayin ganawar tasu, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya nuna cewa, a halin yanzu, ana cikin muhimmin lokacin raya huldar dake tsakanin kasashen biyu. Kasar Sin ta dukufa wajen cimma burinta na "shekaru dari sau biyu", wato kafa wata kasa mai wadata a lokacin cika shekaru dari daya da kafuwar Jam'iyyar Kwaminis ta Kasar Sin a shekarar 2021, da kuma kafa wata kasa ta zamani bisa tsarin gurguzu a lokacin cika shekaru dari da kafuwar jamhuriyar jama'ar kasar Sin a shekarar 2049. A nata bangare kuma, kasar Malaysia tana dukufa kan kafa "sabuwar Malaysia". Cikin shekarun baya bayan nan, firaministan kasar Malaysia ya yi kira da a nemi mulkin kai da kuma inganta hadin gwiwar dake tsakanin kasashen Asiya ta gabas, da kuma tsayawa tsayin daka wajen neman hanyoyin ci gaba da za su dace da halin da kasar take ciki. A matsayinsu na kasashe masu ba da gudummawa ga bunkasuwar yankin Asiya, Sin da Malaysia su kasance muhimman abokan hadin gwiwa, wadanda za su iya samar da damammakin neman ci gaba ga juna. Shi ya sa, ya kamata bangarorin biyu su karfafa shawarwarin dake tsakaninsu, domin ci gaba da raya huldar dake tsakaninsu, ta yadda za su bada gudummawa kan bunkasuwar kasashen Asiya, har ma da kasashen duniya baki daya.

A nasa bangare kuma, Mahathir Bin Mohamad ya bayyana cewa, ziyarar tasa a kasar Sin ta kasance babban matakin da sabuwar gwamnatin kasar Malaysia ta dauka wajen ci gaba da raya huldar abokantaka dake tsakanin kasar Sin da kasar Malaysia. Kasar Sin babbar kasa ce wadda take bada tasiri ga kasa da kasa, kuma ita ce babbar abokiyar ciniki ga kasar Malaysia. Bunkasuwar kasar Sin ba za ta zama kalubale ga kasar Malaysia ba, hadin gwiwar dake tsakanin kasashen biyu ta inganta bunkasuwar kasar Malaysia, kuma yana jin dadin ziyararsa a kasar Sin kwarai da gaske.

Bugu da kari, ya ce, babban ci gaban da kasar Sin ta samu ya kasance abin koyi ga kasar Malaysia, kasarsa tana kuma yabawa matuka kan muhimmin sakamakon da kasar Sin ta cimma kan harkokin masana'antu da cinikayya. Kasar Malaysia tana son koyon fasahohin kasar Sin wajen neman ci gaba, kuma tana maraba da zuwan kamfanonin kasar Sin a kasar Malaysia, ta yadda za'a karfafa hadin gwiwar dake tsakanin kasashen biyu, yayin bada karin tallafi ga al'ummomin kasashen biyu.

Sin da Malaysia suna da zumunci na gargajiya tun shekaru 600 da suka gabata, kuma shirin "Ziri daya da hanya daya" zai ciyar da hadin gwiwar dake tsakanin kasashen yankin gaba. Kasar Malaysia zata halarci shirin cikin himma da kwazo, yayin bada gudummawa yadda ya kamata, saboda tana imanin cewa, shirin zai bada taimako ga bunkasuwar yankin baki daya.

Bugu da kari, ya ce, kasar Sin da kasar Malaysia sun tsaya tsayin daka kan bin hanyoyin neman ci gaba na kansu, lamarin da ya dace da moriyar kansu da na yankin Asiya baki daya. (Maryam)