logo

HAUSA

Amurka: Akwai yuwuwar cimma yarjejeniya kan nukiliyar Iran idan ta ta daukin matakin da ya dace

2021-05-07 12:23:26 CRI

Wani babban jami’in ma’aikatar harkokin wajen Amurka, ya ce kasarsa da Iran na iya komawa yarjejeniyar nukiliyar Iran din cikin makonni masu zuwa, idan Iran ta dauki matakin da ya dace.

Jami’in ya bayyana cewa, tattaunawar da aka yi har zagaye 3 tsakanin kasashen biyu a Vienna, sun taimaka wajen bayyana damarmaki, sai dai ya ce ba a kai ga amincewa da wani abu da ya jibanci yadda za a  farfado da yarjejeniyar ba.

Ya ce idan har Iran na son komawa yarjejeniyar da gaske kamar yadda aka amince da ita, to, za a iya cimma hakan ba tare da bata lokaci ba. sai dai jami’in wanda ya nemi a sakaya sunansa, ya ce ba su san ko Iran ta yanke shawara ba.

Ya kara da cewa, har yanzu da sauran aiki dangane da ka’idojin amincewa da takunkumai da matakan nukiliya, da kuma jadawalin aiwatar da matakan da bangarorin biyu ke bukatar dauka. (Fa’iza Mustapha)

Fa’iza Mustapha