logo

HAUSA

Iran ta sanar da fara tace kaso 20 na sinadarin Uranium a tashar Fordow

2021-01-05 11:34:43 CRI

Hukumar kula da makamashin Atom ta kasar Iran (AEOI) ta sanar a jiya Litinin da dare cewa, za ta farar tace kaso 20 cikin 100 na sinadarin Uranium a tasharta dake Fordow.

Mai magana da yawun hukumar Behrouz Kamalvandi, ya bayyana ta tashar talabijin din kasar cewa, yayin da a baya aka dauki tsawon sa’o’i 24 wajen tace sinadarin, sabbin matakan da masanan kasar suka yi amfani da shi a halin yanzu, zai taimaka wajen kammala aikin cikin sa’o’i 12.

Yanzu haka Iran tana da karfin tace kaso 20 cikin 100 na sinadarin Uranimun, tun bayan da aka haramta mata samun sinadarin a shekarar 2010.

A jiya ne dai aka kaddamar da kaso 20 din da kasar ta tace, a wani bangare na shirin kasar, na yakar takunkumin da aka kakaba mata, wanda ya samu amincewar majalisar dokokin kasar a watan Disamban shekarar 2020.(Ibrahim)

Ibrahim Yaya