logo

HAUSA

Pentagon: Jirgin daukan jiragen saman yakin Amurka zai kasance a yankin gabas ta tsakiya

2021-01-04 15:43:09 CRI

Ma’aikatar tsaron Amurka (Pentagon) ta bayyana cewa, jirgin daukar jiragen saman yakin Amurka mai suna USS Nimitz, zai ci gaba da kasancewa a yankin ruwan gabas ta tsakiya, sakamakon abin da ta kira “barazana daga Iran”, matakin da ke nuna cewa, Amurka ta sauya shawarar da ta yanke a baya, na dawo da jirgin yakin nata zuwa gida.

Amurka da Iran dai, suna ci gaba da musayar kalaman da ka iya haddasa yaki, biyo bayan wani harin makamin roka da aka nufi harabar ofishin jakadancin Amurka dake Bagadaza a ranar 20 ga watan Disamban shekarar da ta gabata

Shugaba Donald Trump na Amurka, ya zargi Iran da kai harin, zargin da Iran din ta musanta. A ranar Larabar da ta gabata, Amurka ta tura jiragen sama masu kai hari da bama-bamai guda biyu kirar B-52H zuwa shiyyar, a matsayin nuna karfi.

A wani sakon mayar da martani da ya wallafa a shafinsa na twita, ministan harkokin wajen Iran, Mohammed Javad Zarif ya ce, maimakon Amurkar ta mayar da hankali wajen yaki da COVID-19 dake ci gaba da halaka ‘yan kasar, Donald Trump da ‘yan kanzaginsa, suna kashe makuden kudade wajen jigilar jiragen saman yaki zuwa yankin. Yana mai cewa, Iran ba ta neman tayar yaki, amma a shirye take ta kare jama’arta, tsaro da muhimman muradunta.(Ibrahim)