logo

HAUSA

A shirye kasar Sin take ta ba da gudummawa ga WTO a matsayinta na kasa mai tasowa

2021-04-08 20:19:04 CRI

Mai magana da yawun ma’aikatar harkokin cinikayya ta kasar Sin Gao Feng, ya bayyana cewa, a shirye kasarsa take, a matsayinta na kasa mai tasowa wadda ke sauke nauyin dake bisa wuyanta, wajen ba da gudummawa ga kungiyar cinikayya ta duniya (WTO) gwargwadon karfinta, kamar yadda yake kunshe cikin manufar daidaiton ‘yanci da wajibci.

Gao Feng wanda ya bayyana haka yayin taron manema labaran da ma’aikatar ta kira, ya ce, duk wani sauye-sauyen yanayi da aka fuskanta daga ketare, har kullum kasar Sin ba za ta juyawa kasashe masu tasowa mambobin WTO baya ba, za kuma ta kare muradunsu.

Gao ya furta kalaman ne, yayin da yake mayar da martani ga kalaman baya-bayan nan da sakatariyar cinikayyar kasa da kasa ta kasar Burtaniya Liz Truss ta yi, game da matsayin kasar Sin na kasa mai tasowa.(Ibrahim)

Ibrahim