logo

HAUSA

Shugaban kasar Sin ya ba da umurnin gaggauta bunkasa aikin noma da kauyuka na zamani

2021-04-08 16:23:27 CRI

Kwanan nan, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya ba da umurni dangane da karfafa hadin gwiwar sassan gabashi da yammacin kasar don samun ci gaba na bai daya, inda ya yi nuni da cewa, aiwatar da hadin gwiwa a tsakanin gabashi da yammacin kasar muhimmiyar manufa ce da gwamnatin kasar ta tsara da nufin daidaita ci gaban sassa daban daban na kasar da tabbatar da bunkasuwarsu ta bai daya. Ya kamata a yi la’akari da sauyin yanayin da ake ciki, kuma a mai da hankali a kan inganta nasarorin da aka cimma ta fannin saukaka fatara da kuma bunkasa kauyuka daga dukkan fannoni, a kokarin da ake yi na karfafa hadin gwiwar sassan gabashi da yammacin kasar.