logo

HAUSA

Yadda kasar Sin ke tallafa wa kasa da kasa wajen rigakafin cutar Covid-19 yana da ma’ana sosai ta fannin bunkasa sana’ar samar da rigakafi

2021-04-08 14:29:51 CRI

Yadda kasar Sin ke tallafa wa kasa da kasa wajen rigakafin cutar Covid-19 yana da ma’ana sosai ta fannin bunkasa sana’ar samar da rigakafi_fororder_微信图片_20210408142917

Shugaban kungiyar masu sana’ar samar da alluran rigakafi ta kasar Sin, Mr. Feng Duojia ya shaidawa taron karawa juna sani na kasa da kasa dangane da rigakafin cutar Covid-19 da aka gudanar ta yanar gizo a ranar 7 ga wata cewa, yadda kasar Sin ke tallafa wa kasa da kasa wajen samar da rigakafin cutar Covid-19, yana da ma’ana sosai ta fannin bunkasa sana’ar samar da rigakafin.

Mr. Feng Duojia ya ce, yanzu haka masu sana’ar hada alluran rigakafi na kasar Sin na fuskantar zarafi, inda ake gaggauta habaka sana’ar tare da inganta nagartar rigakafin da ta samar, wanda hakan ya bukaci masu sana’ar su kara inganta aikinsu, don aza harsashi mai inganci ga fitar da rigakafi kasuwannin duniya.

Ya zuwa ranar 30 ga watan Maris da ya gabata, kasar Sin ta samar da gudummawar rigakafin ga wasu kasashe 80 tare da kungiyoyin kasa da kasa guda uku, baya ga fitar da rigakafin ga kasashe fiye da 40. Ban da haka, kasar Sin ta kuma shiga shirin Covax na hukumar WHO, inda ta yi alkawarin samar da rukuni na farko na rigakafin da suka kai miliyan 10 don biyan bukatun kasashe masu tasowa. Har wa yau, kasar Sin tana goyon bayan kamfanoninta da su yi hadin gwiwa da takwarorinsu na sauran kasashen duniya ta fannonin nazarin rigakafin da yin gwajinsu da kuma samar da su. (Lubabatu Lei)