logo

HAUSA

An kama gomman masu tsattsauran ra’ayi a Habasha

2021-01-25 10:56:42 CRI

Kafar yada labaran kasar Habasha EBC, ta ba da rahoton cewa, an kama gomman wadanda ake zargi da tsattsauran ra’ayi a kasar Habasha a yayin wani gagarumin farmaki da aka kaddamar.

EBC ta ba da rahoton cewa, an kama mutanen da ake zargin ne a wani gagarumin aikin sintiri da aka kaddamar a yankin Dena-Mena dake shiyyar Bale Zone a jahar Oromia ta kasar Habasha.

Jeilan Aman, kwamandan hukumar ‘yan sandan yankin Bale Zone, ya ce an yi nasarar kwato manyan bindigogi da kanana daga hannun mutanen da ake zargin magoya bayan kungiyar masu tsattsauran ra’ayin addini ta cibiyar IS ne.

Cibiyar wacce ake zargin tana yada akidun tsattsauran ra’ayin addini da ayyukan ta’addanci.

Ana zargin cibiyar da cusawa mabiyanta ra’ayin bijirewa dokokin gwamnati ciki har da kin biyan haraji.(Ahmad)

Ahmad Fagam