logo

HAUSA

Jami’an Sudan sun gana da kwararrun AU kan batun tekun Nile

2021-01-10 16:35:12 CRI

Wasu jami’an kasar Sudan da tawagar kwararrun kungiyar tarayyar Afrika AU, a ranar Asabar sun gudanar da taron tattaunawa game da batun gina madatsar ruwan Habasha ta GERD, ma’aikatar noman rani da albarkatun ruwan kasar Sudan ce ta bayyana hakan.

Sanarwar ta bayyana cewa, tawagar wakilan Sudan masu tattauna batun na GERD, wanda ministan noman rani da albarkatun ruwa na Sudan, Yasir Abbas, ke jagoranta, sun gudanar da tattaunawar hadin gwiwar ne da yammacin ranar Asabar tare da tawagar kwararrun AU.

Tattaunawar na zuwa ne a matsayin martani game da kiran da Sudan tayi ga kwararrun kungiyar AU bisa muhimmiyar rawar da za su taka wajen shiga tattaunawar sulhun tsakanin kasashen Sudan, Masar da Habasha domin bayar da gudunmawa a zagaye na biyu na shirye-shiryen samar da yarjejeniyar fahimtar juna wanda kasashen uku suka amince da shi a taron da ya gudana na lokacin baya na bangarori shida.

A cewar sanarwar, taron ya tattauna muhimmancin tsara jadawali game da rawar da kwararrun AU za su taka, ta kara da cewa, Sudan ta jaddada bukatar cewa kamata ya yi AU ta taka muhimmiyar rawa a matsayinta na  shugaba fiye da yadda ta saba takawa a zaman tattaunawar da aka gudanar a lokutan baya.(Ahmad)