logo

HAUSA

UNHCR ta mayar da ‘yan gudun hijirar Habasha wani sabon matsuguni a Sudan

2021-01-06 14:00:29 CRI

Hukumar kula da ‘yan gudun hijira ta MDD, ta sanar da cewa, ta mayar da kashin farko na ‘yan gudun hijirar kasar Habasha da suka kauracewa tashin hankalin dake faruwa a yankin Tigray, zuwa wani sabon wuri a Sudan.

Wata sanarwa da hukumar ta fitar jiya Talata ta bayyana cewa, za ta ci gaba da yiwa sabbin ‘yan gudun hijirar da suka iso kan iyakar Sudan da Habasha rijista. A ‘yan kwanakin da suka gabata na sabuwar shekara, kusan mutane 800 ne suka tsallaka zuwa gabashin Sudan daga yankin Tigray na kasar Habasha.

Wasu rahotanni na cewa, makonni da aka kwashe ana tafka fadace-fadace a Tigray, tsakanin mayakan kwatar ‘yancin yankin da sojojin gwamnati, ya yi sanadiyar mutuwar daruruwan mutane,da wasu dubbai da suka rasa matsugunansu, baya ga miliyoyi da rikicin ya jefa cikin bukatar taimakon jin kai.

Yanzu haka, an kafa tantuna 1,000, wadanda ke iya daukar mutane kusan 5,000, a sabon wurin da aka tsugunar da ‘yan gudun hijirar.

Hukumar ta bayyana cewa, a karshen shekarar 2020, an yi mata alkawarin dala miliyan 40, don tinkarar ayyukan gaggawa a yankin Tigray, amma adadin ya shafi kaso 37 cikin 100 ne kawai na kudaden da ake bukata a kasashen Sudan da Habasha da Djibouti. (Ibrahim)

Ibrahim