logo

HAUSA

Kasar za ta bunkasa kirkire-kirkiren kimiyya a fannin aikin gona nan da shekaru biyar masu zuwa

2021-01-20 11:56:53 CRI

Kasar za ta bunkasa kirkire-kirkiren kimiyya a fannin aikin gona nan da shekaru biyar masu zuwa_fororder_src=http___5b0988e595225.cdn.sohucs.com_images_20171210_63070940ec41483b891e2081135f1f59.jpeg&refer=http___5b0988e595225.cdn.sohucs

Cibiyar nazarin kimiyyar aikin gona ta kasar Sin (CAAS) ta bayyana kudirin kasar na bunkasa kirkire-kirkiren kimiyya da fasahar kere-kere a fannin aikin gona, a wani mataki na raya yankunan karkaka cikin shirinta na raya kasa na shekaru biyar-biyar karo na 14.

Wani rahoto da cibiyar ta fitar, ta ce za ta zage damtse wajen ganin ta kara yin suna a duniya a fannin kimiyyar aikin gona da kirkire-kirkire a fannin kere-kere, da samun nasara a fannin yin kwaskwarima, da yin hadin gwiwa da kasashen duniya, da zama wata cibiyar horas da masu basira, kana cibiyar da za a rika dogaro da sakamakon binckenta.

Rahoton ya kara cewa, cibiyar za ta bayar da muhimmanci, wajen tabbatar da samar da isasshen abinci da kayayyakin amfanin gona cikin shekaru biyar masu zuwa.

Cibiyar ta kuma himmantu, wajen samar da taimako na kimiyya da fasahar kere-kere, a wani mataki na tabbatar da cewa, ana noma sama da tan biliyan 650 na hatsi, domin ganin jama’a da dama ba su sake komawa kangin talauci ba, da kuma yayata farfado da yankunan karkaka.(Ibrahim)

Ibrahim Yaya