logo

HAUSA

Aikin gona na zamani a kauyen Hongguang

2020-09-25 16:18:55 cri

Aikin gona na zamani a kauyen Hongguang

Kauyen Hongguang da ke birnin Changchun na lardin Jilin na kasar Sin ya shahara ne a fannin noman shinkafa a baya, sai dai mazauna kauyen ba su samu wadata ba a sakamakon noman.

Gaba daya mazauna kauyen sun kai sama da dubu daya, kuma fadin gonakinsu ya kai eka 276. A baya, kimanin mazauna kauyen 700 su kan fita cin rani, a yayin da suka ba mazauna dake makwabtaka da kauyensu damar amfani da gonakinsu.

Aikin gona na zamani a kauyen Hongguang

Malam Jin Yingyu ya ce, "Yuan sama da dubu bakwai ne kawai muke samu a shekara a aikin gona." Don haka, tuni shi da uwargidansa sun fita cin rani.

Shugaban kauyen na wancan lokaci Jiang Runzhong ya bayyana cewa, "Kowa ya bar kauyen, ta yaya kauyen zai ci gaba kuma?"

Ya zuwa shekarar 2009, ta hanyar yin amfani da kudaden da gwamnati ta ware, an sayi na'urorin noma tare da fara kafa gonaki na zamani a kauyen.

Malam Jiang Runzhong ya kafa kungiyar hadin kan manoma, kuma ya tara dukkanin gonaki na kauyen, tare da yin hadin gwiwa da kamfanonin aikin gona na zamani.

Aikin gona na zamani a kauyen Hongguang

A cikin 'yan shekarun baya, gaba daya an zuba yuan sama da miliyan 20, don zamanintar da dukkanin gonakin. Baya ga haka, an kuma sayi nau'o'in na'urorin noma na zamani, matakin da ya kara yawan amfani da injuna a fannin ayyukan gona zuwa kimanin kashi 98%.

A cewar malam Jin Yingyu, yanzu yana samun ribar da aka ba shi bisa ga hannayen jari da yake samu a cikin kungiyar a sakamakon gonakinsa da ya bayar, kudin da ya karu da sama da yuan dubu biyar kwatankwacin yadda ya ba saura manoma damar amfani da gonakinsa a baya.(Lubabatu)