logo

HAUSA

Xi Jinping: Ya kamata a kara dora muhimmanci kan batutuwan aikin gona, kauyuka da manoma

2020-12-29 21:13:20 CRI

Xi Jinping: Ya kamata a kara dora muhimmanci kan batutuwan aikin gona, kauyuka da manoma_fororder_微信图片_20201229211202

An gudanar da taron ayyukan kauyuka na kwamitin tsakiyar kasar Sin a jiya Litinin a nan birnin Beijing. A jawabin da ya gabatar yayin da ya halarci taron, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya jaddada cewa, karfafawa tare da fadada nasarorin da aka cimma na kawar da talauci, da inganta aikin farfado da yankunan karkara a dukkan fannoni, da kuma hanzarta zamanantar da aikin gona da yankunan karkara, sune manyan batutuwa da jam’iyyar kwaminis da al’ummar kasar za su dora muhimmanci sosai a kai. Shugaban ya ce, ya dace duk ‘yan jam’iyyar su fahimci muhimmanci da gaggauta gudanar da ayyukan da suka shafi aikin gona, kauyuka da manoma a matakin da kasar take ciki, kana da nacewa wajen warware matsalolin da suke tattare da aikin gona da kauyuka da kuma manoma a matsayin gaba da kome a cikin ayyukan jam’iyyar kwaminis. Ya kamata a yi amfani da karfin jam'iyya da al'ummar kasar, don kara raya yankunan karkara, inganta aikin gona mai inganci, da tabbatar da zaman rayuwa da aiki a yankunan karkara, da kuma wadatar da manoma. (Bilkisu)