Kusan mutanen Habasha 46,000 ne suka tsere yayin da ake rikici a arewacin kasar
2020-12-02 11:30:38 CRI
Hukumar kula da ‘yan gudun hijira ta MDD (UNHCR), ta ce kusan ‘yan kasar Habasha 46,000 ne suka tsere zuwa makwabciyar kasar Sudan, yayin da ake tsaka da rikici tsakanin gwamnati da ‘yan tawaye a yankin Tigray na arewacin kasar.
A karshen makon da ya gabata ne gwamnatin Habasha ta sanar da samun cikakken iko da Mekelle, babban birnin yankin Tigray, lamarin da ya kawo karshen ayyukan dakarun gwamnati.
Hukumar UNHCR wadda ta ce daga ranar Juma’ar da ta gabata, an yi wa ‘yan gudun hijira sama da 2,500 rejista, ta nanata kiran MDD dake cewa, ya kamata dukkan bangarori su gaggauta ba mutanen dake neman taimako da mafaka damar wucewa ta iyakokin kasar da na kasa da kasa cikin aminci ba tare da wata tangarda ba.
A karshen makon da ya gabata ne, hukumar UNHCR da abokan huldarta suka kaddamar da wani shirin tunkarar lamarin jin kai dake da burin taimakawa ‘yan gudun hijira a gabashin Sudan
Shirin da ya hada hukumomin agaji 30 dake aiki tare da gwamnati, na da nufin gaggauta samar da agajin ceton rayuka da suka hada da matsugunai da ruwa da abinci akan kudi dala miliyan 147.
Baya ga haka, hukumar na kira ga hukumomin gwamnatin Habasha, su gaggauta bada damar isa ga ‘yan kasar Eritrea dake gudun hijira a yankin na Tigray, wadanda ta ce suna tsananin bukatar hidimomi da taimakon jin kai. (Fa’iza Mustapha)