Xi Jinping da shugabar Habasha sun taya juna murnar cika shekaru 50 da kafuwar dangantakar diflomasiyya a tsakanin kasashen su
2020-11-24 10:49:47 CRI
Yau Talata, shugaban kasar Sin Xi Jinping da takwarar aikin sa ta kasar Habasha Sahle-Work Zewde sun taya juna murnar cika shekaru 50, da kafuwar dangantakar diflomasiyya a tsakanin kasashen biyu ta wayar tarho.
Xi Jinping ya ce, Sin da Habasha suna da zumunci mai zurfi, kuma cikin ‘yan shekarun nan, kasashen biyu sun kafa dangantakar abokantaka bisa manyan tsare-tsare, yayin da suke karfafa fahimtar juna a tsakaninsu a fannin siyasa, da samun sakamako da dama a fannonin da suka yi hadin gwiwa.
Haka kuma, kasashen biyu sun nuna goyon baya da taimakawa juna, kan batutuwan dake shafar babbar moriyarsu, yayin da suke hada kansu, wajen aiwatar da harkokin kasa da kasa, da na shiyya-shiyya yadda ya kamata.
Ya kara da cewa, bayan barkewar cutar numfashi ta COVID-19, kasar Sin da Habasha, sun nuna wa juna goyon baya da taimako, lamarin da ya kasance abin koyi ta fuskar yin hadin gwiwar yaki da cutar. Kaza lika kasar Sin tana mai da hankali matuka wajen raya dangantar dake tsakaninta da kasar Habasha, tana kuma son yin amfani da wannan dama ta cika shekaru 50 da kafuwar dangantakar diflomasiyya a tsakanin kasashen biyu, wajen aiwatar da sakamakon da aka cimma a taron kolin dandalin FOCAC na birnin Beijing, da kuma taron kolin hadin gwiwar Sin da Afirka na yaki da cutar COVID-19 yadda ya kamata, da kuma karfafa hadin gwiwa bisa shawarar “ziri daya da hanya daya”, domin tallafawa al’ummomin kasashen biyu, da ba da gudummawar karfafa dunkulewar al’ummomin Sin da Afirka bai daya.
A nata bangaren kuma, Sahle-Work Zewde cewa ta yi, cikin shekaru 50 da suka gabata, dangantakar dake tsakanin Sin da Habasha na ci gaba da samun kyautatuwa, bisa ka’idojin hadin gwiwa da fahimtar siyasa, an kuma cimma sakamako da dama, bisa hadin gwiwar dake tsakanin kasashen biyu.
Ta ce yanzu haka, an daga dangantakar dake tsakanin kasashen biyu zuwa dangantakar abokantaka bisa manyan tsare-tsare, a nan gaba kuma, za a ci gaba da zurfafa hadin gwiwar dake tsakanin kasahen biyu bisa fannoni da dama, domin tallafawa al’ummomin kaasshen biyu. Zewde ta ce, tana sa ran yin hadin gwiwa da shugaba Xi Jinping, wajen zurfafa zumuncin gargajiya a tsakanin kasashen biyu, da inganta hadin gwiwar dake tsakaninsu, domin neman ci gaban kasa da wadatar jama’a.
A wannan rana kuma, mamban majalisar gudanarwar kasar Sin, kana ministan harkokin wajen kasar Wang Yi, da mataimakin firaministan kasar Habasha, kana ministan harkokin wajen kasar Demeke Mekonnen, sun taya juna murnar cika shekaru 50 da kafuwar dangantakar diflomasiyya a tsakanin kasahen biyu ta wayar tarho. (Maryam)