Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2009-11-06 16:00:30    
Firaministan kasar Sin ya tashi zuwa kasar Masar don halartar taron ministoci tsakanin Sin da Afrika

cri

Mataimakin ministan ma'aikatar kasuwanci ta kasar Sin Chen Jian ya bayyana cewa, an tabbatar da manufofi 8 da Sin ta dauka kan Afrika. "Kasar Sin ta tabbatar da burin kara samar da tallafi ga kasashen Afrika da kara yawan kayayyakin da Sin ta shigo daga kasashen Afrika ba tare da buga harajin kwastam ba, kuma ana gina yankunan hadin gwiwa na tattalin arziki da ciniki da asibitoci da cibiyoyin rigakafin ciwace-ciwace a Afrika."

Chen Jian ya gabatar da cewa, tallafin da kasar Sin ta samar wa kasashen Afrika ya kawo moriya sosai ga jama'ar kasashen Afrika. Kana a gun taron ministoci na 4, Wen Jiabao zai gabatar da jerin sabbin manufofin karfafa hadin gwiwa a tsakanin Sin da kasashen Afrika. Chen Jian ya fayyace cewa, "A cikin shekaru 3 masu zuwa, za mu kara karfafa hadin gwiwa tare da kasashen Afrika a fannonin makamashi da manyan ayyukan yau da kullum da masana'antu da aikin gona da dai sauransu."

Bugu da kari, a albarkacin lokacin da aka cika shekaru 10 da kafa sabuwar huldar hadin gwiwa a tsakanin kasashen Sin da Masar, Wen Jiabao zai gana da shugaba da firaministan kasar Masar, kuma kasashen biyu za su kulla jerin yarjejeniyoyin hadin gwiwa don ingiza bunkasuwar huldar abokantaka ta hadin gwiwa a tsakaninsu bisa manyan tsare-tsare.(Lami)


1 2 3