Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2009-11-06 16:00:30    
Firaministan kasar Sin ya tashi zuwa kasar Masar don halartar taron ministoci tsakanin Sin da Afrika

cri

"Wannan taro taron ministoci ne da za a yi a karo na farko bayan taron koli da aka yi a birnin Beijing, shugaban kasar Masar Muhammed Hosni Mubarak da wasu shugabannin kasashen Afrika manyan jami'ansu za su halarci bikin bude taron, kana firaministan kasar Sin Wen Jiabao shi ma zai halarci bikin. Babban jigon taron shi ne zurfafa sabuwar huldar abokantaka dake tsakanin Sin da Afrika bisa manyan tsare-tsare da neman bunkasuwa mai dorewa, kuma babban burinsa shi ne dudduba sakamakon da aka samu wajen gudanar da manufofin taron koli na Beijing da tsara shirin hadin gwiwa tsakanin Sin da Afrika a shekaru 3 masu zuwa."

An labarta cewa, a gun taron, kasashen Sin da Afrika za su tattauna batutuwan sauyawar yanayi da rikicin hada-hadar kudi da karancin abinci da makamashi da sauran muhimman batutuwan duniya don cimma matsaya daya da gabatar da "sanarwar Sharm El Sheikh".

A shekaru 3 da suka gabata, shugaban kasar Sin Hu Jintao ya gabatar da sabbin manufofi 8 da gwamnatin Sin ta tsara kan kasashen Afrika, kuma yanzu, an kawo karshen gudanar da wadannan manufofi, za a dudduba sakamakon da aka samu wajen gudanar da su a gun taron.

1 2 3