Har wa yau kuma, rahoton ya bada shawarar cewa, domin samun bunkasuwar tattalin arzikin masana'antun Sin yadda ya kamata kuma cikin tsawon lokaci, kamata ya yi a ci gaba da kyautata tsarin zuba jari, da zuba karin kudi a fannonin zaman rayuwar jama'a, da kimiyya da fasaha, da kiyaye muhalli da sauransu, da gaggauta yin gyare-gyare a fannonin buga haraji da bada tabbacin zaman rayuwar jama'a da sauransu, a kokarin kara biyan bukatun jama'a a gida.(Murtala) 1 2 3
|