Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2009-11-05 21:00:30    
Tattalin arziki na masana'antun kasar Sin na ci gaba da farfadowa

cri

Dadin dadawa kuma, rahoton da aka fitar a wannan rana ya yi nuni da cewa, a halin yanzu dai ana fuskantar wasu matsaloli da kalubaloli a yayin da ake kokarin gudanar da harkokin masana'antu, ciki kuwa har da rashin kudin jarin da aka zuba, da yin tafiyar-hawainiya wajen raya sana'o'i da sauransu. A nasa bangare, shugaban sashin nazarin tattalin arzikin masana'antu na cibiyar nazarin ilimin zaman al'umma ta kasar Sin Mista Jin Bei ya nuna cewa, ya zama wajibi sassa daban-daban su mayar da hankali sosai kan wadannan batutuwa, inda ya ce: "Daga manyan fannoni, muna iya ganin cewa, bayan da muka samu farfadowar tattalin arziki, ya kamata mu yi la'akari kan yadda zamu yi domin ci gaba da samun bunkasuwar tattalin arziki. Irin wannan bunkasuwa tana dogaro kan manufar zaburar da tattalin arziki, shi ya sa kamata ya yi a yi la'akari kan yadda zamu yi domin daidaita wasu matsalolin da suke jawo tsaiko ga habakar tattalin arziki, abun dake gaba da kome a halin yanzu shi ne, yin tsimin makamashi da rage fitar da abubuwa masu gurbata muhalli."

1 2 3