Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2009-11-05 21:00:30    
Tattalin arziki na masana'antun kasar Sin na ci gaba da farfadowa

cri

Ranar 5 ga wata, a nan birnin Beijing, ma'aikatar kula da harkokin masana'antu da sadarwa, da cibiyar nazarin ilimin zaman al'umma ta kasar Sin sun fitar da wani rahoto game da yanayin kaka da bunkasuwar tattalin arziki na masana'antun Sin a shekara ta 2009. A yayin taron da aka fitar da rahoton, jami'an ma'aikatar kula da harkokin masana'antu da sadarwa, gami da kwararru a fannin nazarin tattalin arziki na masana'antu sun bayyana cewa, farfadowar tattalin arzikin masana'antun Sin tana da kwari, haka kuma tattalin arzikin zai ci gaba da bunkasuwa a shekara mai kamawa.

A yayin taron da aka yi a wannan rana, babban injiniya daga ma'aikatar kula da harkokin masana'antu da sadarwa ta kasar Sin Mista Zhu Hongren ya ce, an yi hasashen cewa, a watanni 3 na karshen bana, saurin karuwar tattalin arzikin masana'antun Sin zai kai kashi 16 bisa dari, haka kuma tattalin arzikin masana'antun kasar zai ci gaba da farfadowa: "Gwamnatin kasar Sin tana nan tana ci gaba da aiwatar da manufar kudi yadda ya kamata, a kokarin samar da wani kyakkyawan yanayi ga bunkasuwar tattalin arzikin masana'antu cikin sauri. Gudanar da harkokin sayayya zai ci gaba da taka muhimmiyar rawa a fannin bunkasa masana'antu. A waje guda kuma, ko da yake rikicin ciniki tsakanin kasa da kasa na kara tsanani, sakamakon farfadowar tattalin arzikin duk duniya, harkokin fitar da kayayyakin masana'antu na kasar Sin zuwa ketare zasu kara bunkasuwa a shekara ta 2010."

1 2 3