Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2009-11-05 21:00:23    
Kawance kan aikin karbar harajin kwastam ya kara dungula kasashen gabashin Afirka

cri

An ce, bayan da aka kafa kawance kan aikin karbar harajin kwastam, yawan kudin haraji da aka biya domin yin ciniki a tsakanin kasashen kungiyar EAC ya ragu sosai, haka kuma a watan Janairu mai zuwa, za a daina karbar kudin haraji kan kayayyakin da kasar Kenya ta sayarwa Uganda da Tanzania. Duk da cewar kasashe daban daban su kan dauki manufar kare masana'antunsu ta hanyar kara kudaden haraji ga kayan da ake shigowa da su daga kasashen ketare, amma, kasashen gabashin Afirka na kokarin kauce wa manufar, a game da yadda aka sa yawan cinikin da ke tsakaninsu ya karu sosai. Kamar yadda alkaluma suka nuna cewa, yawan cinikin da aka yi a tsakanin kasashen kungiyar EAC ya karu da kashi 49%, tun daga shekarar 2005 zuwa shekarar 2008. Sa'an nan yawan kayayyakin da kasashen Tanzania da Uganda suka sayar wa sauran kasashen ya ninka sau 2. Bisa la'akari da wani mumunan yanayi dangane da tattalin arziki, wanda ake fama da shi a kewayen duniya, cinikayyar da ake yi a tsakanin kasashen kungiyar EAC ta samar da wani muhalli mai kyau, ta yadda kamfanonin da ke gabashin Afirka za su iya kare kansu daga matsalolin da rikicin hada-hadar kudi ya haddasa.

Ban da ingiza cinikayya, kwancen kungiyar EAC da aikin karbar harajin kwastam ya sa kasashen gabashin Afirka sun kara hada kansu don neman raya tattalin arziki. Kamar yadda masana suke ganin cewa, kawancen ya hada kan kasashen gabashin Afirka sosai, ta yadda aka samar da wata babbar kasuwar da ta kunshi mutane miliyan 120, wadda za ta dinga janyo jari da yawa daga kasashen ketare. (Bello Wang)


1 2 3