Masu sauraro, ko kuna sane da cewa, kungiyar hada kan kasashen gabashin Afirka ta EAC ta kira wani taro a birnin Arusha da ke kasar Tanzania a ranar 31 ga watan da ya gabata, inda manyan jami'an kasashen gabashin Afirka suka tattauna kan yadda za a gyara tsarin kwastam, da kuma inganta kawancen da ya kasance a tsakaninsu, dangane da aikin karbar harajin kwastam. Haka kuma, an ce, an kira taron ne don taya murnar cika shekaru 10 da kafa kungiyar EAC, da kuma cika shekaru 5 da shimfida kawance kan aikin karbar harajin kwastam.
Sa'an nan, kawancen ya kasance babban matakin da kasashen gabashin Afirka suka dauka don neman samun dunkulallen tsari a yankinsu, wanda ya taka muhimmiyar rawa kan ayyuka daban daban, wadanda suka hada da ingiza cinikayya, da raya tattalin arziki, da kuma kara hada kan kasashen yankin waje daya, ta yadda za aza takamammen harsashin da zai kafa wata kasuwar bai daya ta kasashen gabashin Afirka.
1 2 3
|