
Kungiyar EAC ta kunshi kasashe mai membobi 5, da suka hada da Kenya, Tanzania, Uganda, Rwanda, da kuma Burundi, wadda ta shafi mutane miliyan 120, sa'an nan ta samar da wani tattalin arziki da ya kai dala biliyan 60. A watan Janairun shekarar 2005, kungiyar EAC ta kafa kawance dangane da aikin karbar harajin kwastam, wanda da farko ya shafi Kenya, Tanzania,da kuma Uganda kawai. Bayan haka kuma, a watan Yuni na shekarar 2007, kasashen Rwanda da Burundi su ma sun shiga kungiyar EAC, sa'an nan sun halarci kawancen aikin karbar haraji a watan Yuli na shekarar bana.
1 2 3
|