Da aka tabo zance kan bunkasuwar tattalin arziki da kasar Sin za ta samu a shekarar 2010, mista Louis Kuijs yana ganin cewa, bisa yanayin farfadowar tattalin arzikin duniya, kasar Sin za ta kara fitar da kaya zuwa kasashen waje, wato za ta canza hanyoyin da take bi a yayin da take ci gaba da bunkasa ta fuskar tattalin arziki. Bankin duniya ya kyautata zaton cewa, yawan karuwar tattalin arzikin da kasar Sin za ta samu a shekarar 2010 zai kai kusan kashi 8.7 daga cikin dari. Game da haka, mista Louis Kuijs ya ce, 'A shekarar 2010, kasar Sin za ta bi hanyoyi da suka sha bamban da na shekarar da muke ciki wajen samun bunkasuwar tattalin arziki. Da farko, bayan raguwar yawan kayayyakin da take fitarwa zuwa kasashen waje a shekarar bana, kasar Sin za ta samu karuwar yawan kayayyakin da za ta fitar zuwa kasashen waje, wannan zai kasance mai amfani ga bunkasuwar masana'antun kire-kire. Haka kuma masana'antun gidaje za su kara ba da taimako ga bunkasuwar tattalin arziki.'(Danladi) 1 2 3
|