A ran 4 ga wata, ofishin wakilci na bankin duniya da ke kasar Sin ya fitar da sabon rahoto kan tattalin arziki, wanda a kan buga a ko wani bayan watanni uku, inda aka bayyana cewa, bisa shirin sa kaimi ga bunkasuwar tattalin arziki da manyan matakai, kasar Sin za ta cimma makasudinta na samun bunkasuwar tattalin arziki, wato yawan karuwar tattalin arziki da kasar Sin take samarwa a wannan shekara zai kai kashi 8.4 daga cikin dari. Wannan rahoto ya kyautata zaton cewa, kasar Sin za ta kara samun saurin bunkasuwar tattalin arziki a shekarar 2010, hakan kazalika yawan karuwar tattalin arzikin da za ta samu a shekara mai zuwa zai kai kashi 8.7 daga cikin dari.
1 2 3
|