Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2009-11-04 22:06:01    
Bankin duniya ya kyautata zaton cewa, yawan karuwar tattalin arziki da kasar Sin take samarwa a wannan shekara zai kai kashi 8.4 daga cikin dari

cri

Wani kwararre a fannin tattalin arziki na ofishin bankin duniya da ke a kasar Sin Mista Louis Kuijs ya ce, 'Muna ganin cewa, daga kididdgar da muka samu dangane da watanni uku wato watan Yuli, Agusta, da Satumba, muna iya ganin cewa, tattalin arzikin kasar Sin ya farfado daga rikicin kudi na duniya, wannan ya ba tattalin arzikin Sin da na duniya kwarin gwiwa. Ko da yake rikicin kudi na duniya ya dora wa tattalin arzikin kasar Sin mugun tasiri, amma gwamnatin kasar Sin ta aiwatar da babban shirin sa kaimi ga bunkasuwar tattalin arziki, sakamakon haka ta kawar da babbar illa daga rikicin kudi na duniya.' A cikin babban shirinta na sa kaimi ga tattalin arziki, gwamnatin kasar Sin ta ba da rancen kudi mai yawa kan zuba jari, dangane da haka, ana damuwa matsalar yawan tsaban kudaden da ke hannun jama'a, da kuma hauhawar farashin kaya. Game da haka, mista Louis Kuijs ya ce, 'A halin yanzu, bai kamata a damu da hauhawar farashin kaya ba. Muna ganin cewa, darajar hannun jari irin na bogi, da kuma rancen kudi maras inganci suna kawo mana kalubale a halin yanzu. Sakamakon haka, ya kamata a kayyade manufar kudi kafin a daidaita matsaloli a sauran fannonin tatttalin arziki. A fili ne cewa, gwamnatin kasar Sin ta riga ta san wannan matsala, haka kuma ta riga ta dauki wasu matakai domin daidaita matsalar rancen kudi maras inganci.'

1 2 3