Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2009-11-03 21:07:15    
Gwamnatin kasar Sin na fatan masana'antun kasar Sin za su samu adalci a yayin da suke zuba jari a kasashen ketare

cri


'

Ko da yake masana'antun kasar Sin dake zuba jari a kasar Switzerland ba su da yawa a yanzu, amma na yi imani cewa, nan gaba ba da dadewa ba, masana'antun kasar Sin da yawa za su je waje don zuba jari a kasashen Turai, ciki har da Switzerland.'

Mataimakin daraktan kwamitin raya kasa da yin kwaskwarima na kasar Sin Zhang Xiaoqiang ya bayyana cewa, gwamnatin kasar Sin za ta ci gaba da ba da kwarin gwiwa ga masana'antu da suka cika sharuda da su gudanar da hadin gwiwa kan zuba jari a ketare irin na samun moriyar juna da samun nasara tare. A sa'i daya kuma, kasar Sin na fatan bangarori daban daban za su iya nuna adalci ga aikin zuba jari na masana'antun kasar Sin.

'Wadannan masana'antu na kasar Sin suna zuba jari a kasashen ketare bisa kula da bukatun bunkasuwarsu, da ka'idojin kasuwanci, ya kamata a nuna musu girmamawa kamar yadda ake yi ga masana'antu na wasu kasashe. Yunkurin mayar da aikin zuba jarin waje na masana'antun kasar Sin a siyasance, da kuma nuna bambanci gare su, dukkansu suna saba wa hakikanin yanayi, a karshe kuma, za su sheda hasara ga babbar moriyar bangarori daban daban da suke yin hadin gwiwa.' (Bilkisu)
1 2 3