Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2009-11-03 21:07:15    
Gwamnatin kasar Sin na fatan masana'antun kasar Sin za su samu adalci a yayin da suke zuba jari a kasashen ketare

cri

A ranar 3 ga wata a nan birnin Beijing, mataimakin daraktan kwamitin raya kasa da yin kwaskwarima na kasar Sin Zhang Xiaoqiang ya bayyana cewa, a yanayin da ake ciki na raguwar yawan jarin da aka zuba a ketare a duniya sakamakon matsalar kudi da ake fuskanta a yanzu, a watanni tara na farkon shekarar da muke ciki, yawan kudin da masana'antun kasar Sin suka zuba a kasashen ketare ya karu da kashi 1 cikin dari. Ya bayyana cewa, gwamnatin kasar Sin za ta ci gaba da ba da kwarin gwiwa ga masana'antu da suka cika sharuda da su gudanar da hadin gwiwa ta fuskar zuba jari a ketare don samun moriyar juna da nasara ga juna, a waje guda kuma, tana fatan masana'antun kasar Sin za su iya samun adalci a yayin da suke zuba jari a ketare.

Mr. Zhang Xiaoqiang ya yi wannan bayani ne a yayin da ya halarci wani taron tattaunawar hadin gwiwa kan zuba jari a ketare a karo na farko da ake yi a nan kasar Sin. Mr. Zhang Xiaoqiang ya ce, 'Tun daga shekarar da muke ciki, yawan jarin da ake zubawa a waje ya ragu sosai bisa makamanci na bara sakamakon matsalar kudi da ake fuskanta a yanzu. Amma, daga watan Janairu zuwa Satumba na bana, yawan jarin da masana'antun kasar Sin suka zuba a ketare ya kai dalar Amurka biliyan 33, wato ya karu da kashi 1 cikin dari bisa na bara. Ba kawai ya nuna ra'ayin masana'antun kasar Sin na sa himma domin shiga ayyukan gudanar da harkoki na duniya, da kuma habaka hadin gwiwa tsakanin kasa da kasa ba, har ma ya taka muhimmiyar rawa wajen rage mutanen da suke rasa aikin yi, da inganta farfadowar tattalin arziki.'
1 2 3