Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2009-11-03 21:07:15    
Gwamnatin kasar Sin na fatan masana'antun kasar Sin za su samu adalci a yayin da suke zuba jari a kasashen ketare

cri


Ya zuwa karshen shekara ta 2008, yawan jarin waje da masana'antun kasar Sin suka zuba a kasahse da shiyyoyi 174 na duniya ya kai kusan dalar Amurka biliyan 1900. A sa'i daya kuma, sun fi mayar da hankali kan fannonin gyare-gyare da kirkire-kirkire, da manyan ayyuka, da kuma sana'o'in da ke yin amfani da sabbin fasahohi na zamani, ciki har da makamashi, da raya albarkatun ma'adinai, da kayayyakin lantarki na gida, da dai sauransu.

Wani jami'in hukumar kula da bunkasar tattalin arziki ta kasar Switzerland Mr Marco Rhyner ya bayyana cewa, bisa kara yin gyare-gyare da bude kofa ga kasashen waje, da samun bunkasuwar kasar Sin, masana'antun kasar za su kara zuba jari a ketare, kazalika kuma, masana'antun kasar Sin masu yawa za su ziyarci wasu kasashe masu ci gaba don zuba jari.
1 2 3