Kazailka wasu manazarta sun yi nuni da cewa, ko da yake Mr. Karzai zai sake zama shugaban Afghanistan, amma yin magudin zaben a zagayen farko ya lalata surar gwamnatin da ke karkashin shugabancin Mr. Karzai. Sa'an nan kuma, janye jikin Mr. Abdullah daga zagaye na biyu na zaben ya haddasa shakku kan halaltaccen matsayin sabuwar gwamnatin Afghanistan. Yanzu Mr. Karzai na bukatar hada kai da Mr. Abdullah wajen kafa gwamnatin hadin gwiwa, da yin kokarin ganin sabuwar gwamnati ta samu amincewa. Amurka kuma tana shiga tsakani a wannan fanni. A ganin Amurka, sabuwar gwamantin Afghanistan da ke samun amincewa daga jama'a da kuma nagartacciyar kwarewar mulkin kasa tana da matukar muhimmanci a gare ta wajen gudanar da manyan tsare-tsarenta na yaki da 'yan ta'adda a Afghanistan.
Yanzu Mr. Karzai da Mr. Abdullah ba su samu ra'ayi daya a game da kafa gwamnatin hadin gwiwa ba tukuna. Nan gaba ko Mr. Karzai zai kafa gwamnatin hadin gwiwa ko a'a, ko kuma za a samu nasarar kafa gwamnatin hadin gwiwa ko a'a, ana sa ido kan hakan.(Tasallah) 1 2 3
|