Bayan da aka bayyana Mr. Karzai a matsayin sabon shugaban Afghanistan, kasashen duniya sun yi maraba da wannan. Ban Ki-moon, babban sakataren Majalisar Dinkin Duniya da ya kai ziyarar ba zata a Afghanistan a wannan rana, ya bayyana cewa, babban zaben da aka yi a wannan karo ya ba Afghanistan wahala, tilas ne ta koyi fasahohi daga wajensa. Yanzu Afghanistan na fuskantar tsananin kalubaloli. Ta haka tilas ne sabon shugaban kasar ya kafa gwamnatin da ke biyan bukatun jama'ar Afghanistan da na kasashen duniya duka. Haka kuma, a ran nan, ba tare da bata lokaci ba ofishin jakadanci na kasar Amurka a Afghanistan ya taya Mr. Karzai murnar sake zama shugaban kasar, ya kuma nuna fatansa na hada gwiwa da Mr. Karzai. Dadin dadawa kuma, kasar Birtaniya ita ma ta yi wa Mr. Karzai murna.
Manazarta sun nuna cewa, soke zagaye na biyu na zaben zabi ne mafi dacewa ga Afghanistan a halin yanzu, shi ya sa ba a yi suka sosai kan wannan kuduri ba. Idan an yi zagaye na biyu na zaben bisa shirin da aka tsara, to, Afghanistan za ta fuskanci kalubaloli da yawa a fannonin siyasa da lalacewar halin tsaro da kuma zirga-zirga a yankunan karkara a sakamakon kusantowar lokacin hunturu.
1 2 3
|