Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2009-11-03 21:07:06    
Karzai zai ci gaba da zama shugaban Afghanistan

cri

Ran 2 ga wata, kwamitin harkokin zabe na kasar Afghanistan mai zaman kansa ya soke zagaye na biyu na zaben shugaban kasar da aka shirya yi a ran 7 ga wata, kuma ya bayyana shugaba Hamid Karzai a matsayin wanda ya lashe zagayen farko na zaben, ta haka ya sami nasarar sake zama shugaban Afghanistan.

Azizullah Ludin, shugaban kwamitin ya bayyana a wani taron manema labaru cewa, saboda malam Karzai ya lashe zagayen farko na zaben, kuma ya kasance dan takara daya kacal a cikin zagaye na biyu na zaben, shi ya sa kwamitin ya soke zagaye na 2 na zaben. Sa'an nan malam Karzai ya zama sabon shugaban kasar. Malam Ludin ya kara da cewa, dalilin da ya sa haka shi ne domin magance matsalar bata lokaci, har ma jama'ar kasar sun yi sadaukarwa a sakamakon sabon zagaye na zaben. Sa'an nan kuma, kada kuri'a kan dan takara daya kacal zai haddasa shakku a kan halaltaccen matsayin sabon shugaban kasar.

Ran 20 ga watan jiya, kwamitin harkokin zabe na Afghanistan mai zaman kansa ya sanar da cewa, saboda dukkan 'yan takara 2 ba su samu kuri'un da yawansu ya wuce rabi a cikin zagayen farko na zaben ba. Bisa kundin tsarin mulkin Afghanistan, an ce, 'yan takara 2 da ke kan gaba a fannin samun kuri'u wato Mr. Karzai da Mr. Abdullah za su shiga zagaye na biyu. Amma a ran 1 ga wata, Mr. Abdullah ya sanar da janye jikinsa daga zagaye na biyu na zaben. Ta haka Mr. Karzai ya zama dan takara daya kacal. Kafin wannan, kwamitin harkokin zabe na Afghanistan mai zaman kansa ya taba bayyana cewa, ko da Mr. Abdullah ya janye jiki, za a yi zaben kasar na zagaye na biyu.

1 2 3