Haka kuma, a ran 18 ga wata, gwamnatocin kasashen Amurka da Ingila sun bayar da sanarwoyi, inda dukkansu suka bayyana cewa, ba ruwansu da matsalolin kai farmaki da suka auku a lardin Sistan Baluchestan na kasar Iran.
Bugu da kari kuma, bisa labarin da gidan talibijin na watsa labaru na Iran ya bayar, an ce, a ran 18 ga wata, kungiyar "Jundallah" wadda ke nuna adawa da gwamnatin Iran ta sanar da cewa, ita ce ta shirya farmaki irin na kunar bakin wake a lardin Sistan Baluchestan. Wannan kungiya ta kan fito a yankunan da ke bakin iyakar da ke tsakanin Iran da Pakistan. Yanzu gwamnatocin Iran da Pakistan sun riga sun tabbatar da cewa, ita kungiya ce ta nuna ta'addanci. Wannan kungiyar "Jundallah" ta taba ta da matsalolin kai farmaki har sau da dama a lardin Sistan Baluchestan na kasar Iran, inda aka haddasa mutuwa da kuma raunata mutane da yawa. 1 2 3
|