Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2009-10-19 21:23:40    
An samu matsalar kai farmaki irin ta kunar bakin wake mai tsanani sosai a Iran

cri

A ran 18 ga wata, an samu wata matsalar kai farmaki irin ta kunar bakin wake a lardin Sistan Baluchestan na kasar Iran, inda aka haddasa mutuwar mutane 35, ciki har da manyan hafsoshi 2 na rundunar tsaron juyin juya hali ta Musulunci ta kasar Iran, wasu mutane 28 suka kuma jakkata. Wannan matsalar kai farmaki ce mafi tsanani da ta auku a kasar Iran bayan da aka kawo karshen yakin Iran da Iraki a shekarar 1988.

Bisa labarin da kamfanin dillancin labaru na Iran ya bayar a ran 18 ga wata, an ce, da misalin karfe 8 na wannan rana da safe, an shirya wani taron dattawa a birnin Pishin na lardin Sistan Baluchestan da ke gabashin kasar Iran. A yayin taron, wani mutum ya ta da boma-bomai da ya kulla a jikinsa. Sakamakon haka, janar Nourali Shoushtari, mataimakin babban kwamandan sojojin kasa da Rajabali Mohammadzadeh, kwamandan sashen lardin Sistan Baluchestan na rundunar tsaron juyin juya hali ta Musulunci ta kasar Iran da wasu manyan hafsoshi tare da wasu dattawa sun mutu.

Bisa wani labari daban da gidan talibijin na kasar Iran ya bayar, an ce, an samu matsalolin kai farmaki biyu a wannan rana. A lokacin da ake samun matsalar kai farmaki irin ta kunar bakin wake a lardin Sistan Baluchestan, an kuma kai farmaki kan wasu motoci masu dauke da manyan hafsoshin Iran lokacin da suke kan hanyar zuwa wurin taron, inda aka yi sanadiyyar raunata wasu hafsoshi.

1 2 3