A gun taron majalisar ministocin kasar da aka shirya a wannan rana da dare, Mr. Mahmoud Ahmadinejad, shugaban kasar Iran ya nemi a gano wadanda suka shirya wadannan matsaloli cikin sauri, kuma a yanke musu hukunci. Ya kuma nemi gwamnatin kasar Pakistan da ta dauki matakin cafke wadanda suka shirya wadannan matsaloli ba tare da bata lokaci ba. Mr. Mahmoud Ahmadinejad ya ce, "Mun sani, wasu 'yan sandan kasar Pakistan suna yin hadin gwiwa tare da 'yan ta'adda wadanda suka shirya wadannan matsalolin kai farmaki, sabo da haka, muna da ikon gabatar da irin wannan bukata."
A waje daya, rundunar tsaron juyin juya hali ta Musulunci ta Iran ta bayar da wata sanarwa, inda ta zargi rukunonin kasashen waje da suke da nasaba da kasar Amurka da cewa suna da hannu cikin wadannan matsalolin kai farmaki. Gidan talibijin na kasar Iran ya kuma yi amfani da wata majiya da cewa, gwamnatin kasar Ingila ta sa hannu cikin wadannan matsaloli kai tsaye, har ma ta dauki tare da tattara 'yan ta'adda da kuma samar musu makamai. A gun wani taron manema labaru da aka shirya a wannan rana da yamma, janar Mohammad Pakpur, kwamandan sojojin kasa na rundunar tsaron juyin yuya hali ta Musulunci ta Iran ya bayyana cewa, rundunar sojan tsaron juyin juya hali ta Musulunci ta Iran za ta mai da martani ga rundunonin nuna ta'addanci na cikin gida da na waje.
1 2 3
|