Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2009-10-19 11:35:30    
Ana fatan kasar Sin za ta iya zama a gaba a duniya a fannin tattalin arziki

cri

Halin da tattalin arzikin kasar Sin ke ciki yana jawo hankalin nagartattun mutane wadanda suke tafiyar da harkokin tattalin arziki a duniya. Mr. Maurice Levy, shugaba kuma babban jami'in zartaswa na kamfanin Publicis Group na kasar Faransa wanda ya halarci taron shekara-shekara na Davos da aka yi a birnin Dalian a karo na biyu ya ce, matakan ingiza ci gaban tattalin arziki da kasar Sin ta dauka a 'yan shekarun baya, da kuma kwararan matakan tinkarar matsalar kudi da ta dauka su abubuwa ne da ya kamata sauran kasashen duniya su koya. Mr. Maurice Levy ya ce, ""Dalilin da ya sa na zo nan shi ne koyon ilmi. Sabo da kasar Sin ta samu kyakkyawan makin da ba a safai a kan gan shi ba ta fuskar karuwar tattalin arziki. Ban taba ganin irin wannan ci gaba ba a kasashen yammacin duniya. Ina son sanin mene ne ya sa kasar Sin ta zama wata kasa na-gari sosai."

A hakika dai, lokacin da ake bunkasa tattalin arziki bai daya a duk duniya, sauran kasashen duniya suna kuma samun moriya daga ci gaban da kasar Sin ta samu cikin sauri a fannin tattalin arziki. Mr. Zorigt Dashdorj, mataimakin ministan hakar ma'adinai na kasar Mongoliya wanda ya kuma halarci wannan taro ya gaya wa wakilinmu cewa, "Ci gaban da kasar Sin ta samu a fannin tattalin arziki ya kuma kawo moriya ga karuwar tattalin arzikinmu. Dangane da kasar Mongoliya, abin da ya kamata mu yi nazari shi ne yaya za mu iya hawa kan wani sabon mataki wajen kara darajar kayayyakinmu, kuma yaya za mu iya sa kaimi ga kamfanonin kasashen Rasha da Sin da su kafa masana'antun sarrafa ma'adinai irin na karfe da na tagulla a kasar Mongoliya. Sabo da za su iya samar da karin guraban aikin yi ga 'yan kwadagon kasarmu, kuma za su iya kawo moriya ga kokarin raya masana'antu da zamanintar da kasar Mongoliya."

Kasar Sin ta samu nasara sosai wajen tinkarar matsalar kudi ta duniya. Sabo da haka, wasu mutane suna ganin cewa, kasar Sin za ta iya zama kasar da ke iya jagorancin sauran kasashen duniya wajen fama da matsalar. Game da irin wannan ra'ayi, Mr. Sha Zukang, babban sakataren majalisar dinkin duniya yana ganin cewa, kasar Sin ba ta da irin wannan karfi tukuna. Mr. Sha ya ce, "Bisa kididdigar da majalisar dinkin duniya ta yi, har yanzu kasar Sin kasa ce da ba ta kai matsayin matsakaicin karfi ba a duniya. Sakamakon haka, idan ana son ta shugabanci tattalin arzikin duniya, abu ne mai wuya. A ganina, a cikin dogon lokaci mai zuwa, kasar Amurka da kasashen Turai za su ci gaba da zama muhimmin karfin ci gaban tattalin arzikin duniya."

Mr. Zhang Xiaoqiang, mataimakin shugaban kwamitin ci gaba da yin gyare-gyare na kasar Sin ya amince da ra'ayin Mr. Sha Zukang. Mr. Zhang ya ce, "Kasar Sin kasa ce da yawan mutanenta ya fi yawa a duniya, wato yawansu ya kai kashi 1 cikin kashi 6 bisa na jimillar yawan mutanen duniya. A waje daya, jimillar tattalin arzikinmu tana da girma kwarai, wato yawanta ya kai dalar Amurka biliyan dubu 4 a shekarar da ta gabata, kuma zai samu karuwa da kashi 8 cikin kashi dari a shekarar da muke ciki. Tabbas ne kasar Sin za ta taka muhimmiyar rawa wajen sa kaimi ga ci gaban tattalin arziki da zaman al'umma na duk duniya. Amma har yanzu, kasar Sin kasa ce mai tasowa wadda matsakaicin kudin shiga da kowane mutum ke samu ya yi kadan. Sabo da haka, dole ne kasar Sin ta bi wata doguwar hanyar neman ci gaba a nan gaba."


1 2 3