Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2009-10-19 11:35:30    
Ana fatan kasar Sin za ta iya zama a gaba a duniya a fannin tattalin arziki

cri

Wani muhimmin dalilin da ya sa aka jawo 'yan siyasa da kwararru da nagartattun mutane wadanda suke tafiyar da harkokin tattalin arziki suka halarci wanann taro shi ne farfadowar tattalin arzikin kasar Sin cikin sauri ya sa sun sani, cewar da akwai fatar cin nasarar tinkarar matsalar kudi ta duniya. A yayin bikin kaddamar da taron, Mr. Wen Jiabao, firayin ministan kasar Sin ya bayyana cewa, yanzu tattalin arzikin duniya ya soma samun farfadowa a kai a kai. Matakan ingiza ci gaban tattalin arziki da kasar Sin ta dauka domin tinkarar matsalar kudi ta duniya sun kuma soma taka rawarsu. Ya zuwa yanzu, kasar Sin ta riga ta kayyade raguwar tattalin arziki. Saurin ci gaban tattalin arziki da kasar Sin ta samu a farkon rabin shekarar da ake ciki ya kai fiye da kashi 7 cikin kashi dari. Kuma saurin zuba jari ya kuma samu karuwa cikn sauri. A waje daya, yawan karin guraban aikin yi da aka samar a garurruka da birane a cikin farkon watanni 7 na shekarar da ake ciki ya kai fiye da miliyan 6 da dubu dari 6. Kuma yawan kudin shiga da jama'a ke samu yana ta karuwa. Mr. Wen Jiabao ya ce, "A lokacin da tattalin arzikin duniya ke raguwa sosai, ba abin ne mai sauki ba samun irin wannan ci gaba. Wannan kyakkyawan sakamako ba ya fado daga sararin sama ne kawai ba, amma ya zo ne sabo da gwamnati da jama'ar kasar Sin sun dauki matakan kasafin kudi da manufofin kudi bisa hakikanin halin da kasar ke ciki, kuma ta aiwatar da jerin manufofi wajen tinkarar matsalar kudi ta duniya."

A ranar da ake kaddamar da wannan taro, hukumar kididdiga ta kasar Sin ta sanar da jerin kididdigar tattalin arziki. Wannan kididdiga ta bayyana cewa, ana ta karfafa tushen tattalin arzikin kasar Sin. Kuma yiyuwar cimma burinta na karuwar tattalin arziki da kashi 8 cikin kashi dari tana samun tabbatatuwa.

Amma a waje daya, har yanzu kasar Sin tana fuskantar kalubale iri iri a nan gaba wajen bunkasa tattalin arziki. Game da irin wadannan kalubale, Mr. Wen Jiabao ya kara da cewa, "Za mu ci gaba da sanya aikin tabbatar da samun ci gaban tattalin arziki ba tare da wani tangarda ba a gaban kome. Kuma za mu ci gaba da tsayawa tsayin daka kan matsayin aiwatar da manufofin kasafin kudi cikin hali mai yakini da kuma manufofin kudi masu sassauci da suka dace. A waje daya, za mu dinga wadata da kuma kyautata jerin shirye-shirye daga dukkan fannoni da kuma gano da warware sabbin matsalolin da kila za su bullo a nan gaba ta fuskar tattalin arziki cikin lokaci. Sannan za mu yi kokarin tsara manufofin da za su iya kara dacewa da hakikanin halin da ake ciki cikin lokaci."

1 2 3