Tun daga ran 10 zuwa ran 12 ga watan Satumba, an yi taron shekara-shekara na lokacin zafi a karo na uku dangane da sabbin kasashe masu tasowa a fannin tattalin arzikin duniya a birnin Dalian da ke arewacin kasar Sin. A yayin taron, makomar tattalin arzikin kasar Sin da tasirin da kasar Sin ke kawo wa sauran kasashen duniya sun zama batutuwan da ke jawo hankalin mahalarta taron.
Muhimmin taken wannan taro shi ne "Yin kokarin sake samun ci gaba". 'Yan siyasa da kwararru da masu tafiyar da harkokin tattalin arziki fiye da dubu 1 da dari 4 da suka zo daga kasashe da yankuna fiye da 180 sun halarci wannan taro, inda suka yi musayar ra'ayoyinsu kan huldodi a tsakanin kirkire-kirkire da kimiyya da fasaha, kuma a tsakanin aikin kawo arziki da kashe kudi ba tare da wani tangarda ba, kuma a tsakanin harkokin kudi da zuba jari da dai makamatansu.
A ganin Dr. Mahmoud Mohieldin, ministan kula da harkokin zuba jari na kasar Masar, wannan taro ba ma kawai ya zama wani dandalin da mahalarta taron suke samun bayanai game da halin da ake ciki ta fuskar tattalin arzikin kasashen duniya ba, har ma ya zama wani dandalin da mahalarta taron suke sanin kasar Sin ta yau. Malam Mohildin ya bayyana cikin harshen Larabci cewa, "Shirya wannan taro a kasar Sin yana da muhimmiyar ma'ana. Dandalin tattaunawar tattalin arzikin duniya ya kan bayar da gudummawa sosai ga wadanda suke son sanin halin da ake ciki a duniya ta fuskar tattalin arziki. Yanzu an shirya taron wannan dandali a kasar Sin, kuma an bayar da ra'ayoyi game da bunkasuwar tattalin arziki da zaman al'ummar kasar Sin. A waje daya, a yayin taron, mun fahimta kuma san babban ci gaban da kasar Sin ta samu. Wannan zai yi matukar amfani ga kokarin raya huldar da ke tsakanin kasar Sin da sauran kasashen duniya, ciki har da kasar Masar."
1 2 3
|