Jihar Xinjiang mai cin gashin kanta ta Uygur ta kasance jiha mafi fadi a kasar Sin. A cikin shekaru da dama da suka wuce, jama'ar Xinjiang 'yan kabilu daban daban suna hadin kai da juna da taimakon juna, kuma suna zaman jituwa da juna, kuma tattalin arzikin jihar ya bunkasa cikin sauri, musamman ma a cikin 'yan shekarun da suka gabata, an tabbatar da bunkasuwar tattalin arziki fiye da kashi 10% a jihar.
A lokacin murnar cika shekaru 60 da kafuwar jamhuriyar jama'ar Sin, a birnin Urumqi, hedkwatar jihar Xinjiang, an kawatar da titunan birnin, kowane kanti ya daga tutar kasar Sin, Ge Hongming, wani mazaunin birnin ya ce,"akwai murna da farin ciki da fatan alheri, iyalina ba mu iya haduwa a kowace rana, amma yanzu muna iya haduwa muna taya murnar ranar kasarmu." 1 2 3
|